ZAIZAYAR KASA DA ILLOLINTA

Spread the love

Ramukan kasa da mutane ke tonawa domin ayyukan gidaje da tituna, su kan zamo alakakai idan aka dauki tsawon lokaci. Irin wadannan ayyuka kan haddasa zaizaiyar kasa wadda kan kasance matsala babba ga gonaki ko guraben zama. Sau da yawa ba’a la’akari da kusancin irin waddannan ramuka da hanyoyi, tituna ko kuma dazuka dake kare mummunan yanayi.

Ayyukan saran kasa, wadanda wasu dubban mutane ke dogara dashi a matsayin sana’a ta kasance ana yinta ne ba tare da wani tsari ko ka’ida da gwamnati ta gindaya ba, domin hakane ake samu matsaloli da kanyi wuyar warwarewa. Idan irin wadannan ramuka suka jawo matsalar zai zaiyar kasa, gwamnatoci da al’umma sune ke shan wahala wajen biyan diyya do neman hanyoyin magance matsalar wadda kan lakume miliyoyin kudi.